'Yan tawayen Syria sun kai gagarumin farmaki a Aleppo
'Yan tawayen Syria sun kaddamar da gagarumin farmaki kan dakarun gwamnatin kasar da nufin karbe wasu yankunan birnin Aleppo da dakarun ke rike da su.
Wallafawa ranar:
Tun a ranar 17 ga watan Yuli ne, dakarun shugaban Syria Bashar al-Assad suka kewaye yankunan Aleppo da ‘yan tawayen ke rike da su.
Dakarun dai sun datse hanyar Castello wadda ita ce, babbar hanyar shigar da kayayyaki ga ‘yan tawayen a Aleppo.
A cikin sanarwar da suka fitar, kungiyoyin mayakan da suka hada da Ahrar al- Sham da Jabhat Fateh al- Sham sun ce, sun fara yaki don ganin sun sake bude wata sabuwar hanyar isar musu da kayayyaki.
Kungiyar Fateh al Sham dai ita ce, ta kaddamar da hare-haren bama-bamai kan dakarun gwamnatin da ke aiki a yankin Suburban Rashidin wanda ke kudu maso yammacin Aleppo.
Kananan yara uku na cikin mutane 11 da suka rasa rayukansu a hare-haren rokan da ‘yan tawayen suka harba daga Rashidin zuwa Hamdaniyeh da ke yankin yammacin birnin, inda wasu dakarun gwamnatin ke rike da shi.
An kaddamar da sauran hare-haren ne a Ramussa da ke kudancin Aleppo.
Kungiyar da ke sa ido kan Syria ta ce, za a dauki tsawon lokaci ana gwabza yaki mai zafi tsakanin bangarorin biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu