Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton na shirin sanar da mataimakinta a takarar Amurka

Yau ake saran ‘yar takarar jam’iyyar Democrat a zaben shugabancin kasar Amurka Hillary Clinton, za ta bayyana wanda zai mara mata baya a matsayin mataimaki kafin babban taron jam’iyyar da za a fara ranar litinin.

'Yar takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat Hillary Clinon
'Yar takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat Hillary Clinon REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Rahotanni sun ce Sanata Tim Kaine, dan majalisar dattawa daga jihar Virginia da ya fito daga cikin masu magana da harshen Spaniyanci ke gaba cikin wadanda ake saran dauka.

Ana kallon Sanata Kaine a matsayin wanda zai samar wa Clinton karin magoya baya a jiharsu da kuma asalin mutanen da ke magana da harshen Spaniyanci da ke kasar.

Sauran wadanda ke neman kujerar sun hada da sakataren noma Tom Vilsack daga jihar Pensylvania da sakataren kwadago Thomas Perez daga Latino.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.