Isa ga babban shafi
Libya

ISIL ta yi karfi a Libya

Mayakan kungiyar ISIL na ci gaba da kafa sansanoni a Libya bayan sun gudo daga Syria da Iraqi sakamakon matsin lamba da suke fuskanta na hare hare da kuma tsaurara matakan tsaro akan iyakokin kasashen.

Mayakan Daesh da ke da'awar Jihadi a Libya da Syria da Iraqi
Mayakan Daesh da ke da'awar Jihadi a Libya da Syria da Iraqi REUTERS/Stringer
Talla

Cibiyar kula da yawon bude ido a Libya ta ce, kimanin mayakan ISIL dubu 10 ke zaune a kasar.

Rahotanni sun ce, daruruwan mayakan ISIL da ke ikirarin jihadi ke ci gaba da kwarara cikin Libya don samun damar cin karansu ba babbaka.

Mayakan na samun karfi ne a Libya saboda yadda kasar ke fama da matsalar tsaro gami da rashin tsayayyiyar gwamnati.

Tun lokacin da aka kifar da gwamnatin Kanal Ghaddafi kasar Libya ta fada cikin wani mummunan hali duk da gwargwadon arzikin da Allah da ya ba wa kasar na fetir.

ISIL ta kafa kananan sansanoni a waurare da dama a Libya da suka hada da Benghazi da Tripoli.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa, akalla akwai mayakan IS dubu uku da ke zaune a Libya kuma suna shigar da mutane cikin kungiyar.

A bangare guda, cibiyar kula da yawon bude ido ta kasar ta ce, a halin yanzu adadin mayakan sun zarce dubu 10 a Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.