Isa ga babban shafi
Libya

An kashe Sojojin Libya 34 a Sirte

Akalla sojojin gwamantin hadin kan kasar Libya 34 aka tababtar da mutuwarsu a fafatawar da suka yi da kungiyar mayakan IS a Sirte, mahaifar tsohon shugaban kasa Marigayi Kanal Muammar Ghaddafi.

Dakarun da ke biyayya ga gwamnatin Libya
Dakarun da ke biyayya ga gwamnatin Libya REUTERS/Stringer
Talla

Wani jami'in lafiya a garin ya ce wadanda suka samu raunuka sun zarce 100.

Wannan ya biyo bayan korar mayakan IS ne da dakarun gwamnatin hadin kan kasar suka yi a watannin da suka gabata inda yanzu IS ta sake kaddamar da hare hare kan dakarun gwamnati domin sake kwato garin na Sirte.

Wannan dai shi ne adadi mafi muni da aka kashe dakarun kasar tun kaddamar da farmaki akan IS a Sirte a watan Mayu.

Amma babu wani cikakken bayani akan adadin mayakan IS da aka kashe a musayar wutar tsakaninsu da dakarun Gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.