Isa ga babban shafi
AFGHANISTAN

Amurka za ta bar dakaru 8,400 a Afghanistan a 2017

Shugaba Barack Obama ya ce sojojin Amurka dubu 8 da 400 za su ci gaba da kasancewa a Afhganistan har zuwa shekara ta 2017 sabanin dubu 5 da 500 kamar yadda Amurkan ta sanar da farko.

Shugaba Obama  Amurka
Shugaba Obama Amurka REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Duk da cewa Obama ya yi alkawarin janye illahirin sojojin kasar daga Afghanistan a karshen 2014, to sai dai ga alamu ya canza matsayi saboda dalilai na tsaro.

Yanzu haka dai kungiyar Taliban na ci gaba da fadada hare-harenta a cikin kasar ta Afghanistan, wata alama da ke kara nuni da raunin da dakarun kasar ke da shi domin tabbatar da tsaro matukar dai Amurka ta janye.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.