Isa ga babban shafi

‘Yan Hazaras na zanga-zanga a Afghanistan

Dubban ‘Yan kabilar Hazaras mafi yawancinsu ‘Yan Shi’a sun mammaye birnin Kabul suna zanga-zangar neman dawo da hanyar wutar lantarki zuwa yankinsu daga kasashen da ke tsakiyar yankin Asia.

'Yan kabilar Hazaras sun mamaye birnin Kabul
'Yan kabilar Hazaras sun mamaye birnin Kabul WAKIL KOHSAR / AFP
Talla

An tsaurara tsaro a Kabul tare da rufe manyan hanyoyin babban birnin na Afghanistan bayan da ‘yan kabilar Hazaras suka doshi zuwa fadar shugaban kasa suna zanga-zangar neman a ratso da hanyar lantarki zuwa yankinsu karkashin tsarin wadata lantarki a kasasghen Afghanistan da Pakistan.

Shugaban ‘Yan kabilar Hazara ne Dawood Naji ke jagorantar zangar-zangar zuwa fadar gwamnatin Ashraf Gani.

Tsarin samar da lantarki dai ya shafi kasashen Turkmenistan da Uzbekistan da Tajikistan zuwa Afghanistan da Pakistan.

Da farko an tsara biyo da lantarkin zuwa Bamiyan yankin ‘yan kabilar Hazaras mafi amma daga baya gwamnatin Afghanistan ta sauya tunani zuwa ratso da lantarkin ta arewacin Kabul saboda ya fi kusa kuma zai sa a rage kudaden da za a kashe ga aikin lantarkin.

Amma ‘yan hazara da ke zanga-zangar na ganin an sauya tunani ne saboda an mayar da su saniyar ware.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.