Colombia ta sasanta da ‘Yan tawayen FARC
Gwamnatin Kasar Colombia ta sanar da kulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta din-din-din tsakaninta da ‘Yan Tawayen FARC domin kawo karshen yakin basasan da aka kwashe shekaru 50 ana yi a kasar.
Wallafawa ranar:
A sanarwar da bangarorin biyu suka rabawa manema labarai sun ce sun yi nasarar kulla yarjejeniyar kawo karshen duk wani tashin hankali a kasar.
Ana sa ran yau Alhamis shugaban kasa Juan Manuel Carlos da kwamandan ‘Yan Tawayen Timoleon Jimenez za su bayyana nasarar da aka samu a wani biki da wasu shugabannin kasashen duniya da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya za su halarta.
Tun a 1960 Colombia ke rikici da ‘Yan tawayen FARC, wanda ya salwantar da rayukan mutane sama da dubu dari da hamsim tare da raba sama da mutane Miliyan bakwai da gidajensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu