Isa ga babban shafi
UN

Yau ne ranar kare zabaya ta duniya

Yau ne ranar fafutukar kare zabaya ta duniya da Majalisar dinkin duniya ta ware domin fadakarwa da kuma  kokarin kawo sauyi a zamansu a kasashen kudancin Afrika.

Ikponwosa Ero,babar jami'ar hukumar kare hakkin dan adam da kuma kare zabaya a duniya
Ikponwosa Ero,babar jami'ar hukumar kare hakkin dan adam da kuma kare zabaya a duniya AFP/Amos Gumulira
Talla

Azabtarwa da muzgunawa da kisa na daga cikin matsallolin da zabaya ke fuskanta a wasu kasashen duniya.

Shekara daya kenan da Majalisar dinkin duniya ta samar da wannan ranar ta kare zabaya daga fuskantar musgunawa musaman a kasashen kudancin sahara da kasashen da suka hada da Tanzania da Jamhuriyar demokradiya Congo da Burundi da Malawi da kuma Cote d’ivoire.

Babbar jami’ar hukumar kare hakkokin bil Adama da kuma kare zabaya a duniya, Ikponwosa Ero,  wadda ita ma zabaya ce kuma 'yar asalin Najeriya ta sanar da wani  sakamakon bicinke da ke  nuna yadda ake a muzugunawa mutanen da ke da wannan lalura.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.