Isa ga babban shafi
Pakistan

Taliban za ta zabi sabon shugabanta

Majiyoyin tsaron Pakistan sun tabbatar wa kamafanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, wani jirgin saman Amurka mara matuki ya kashe shugaban Taliban Mullah Akhtar yayin da kungiyar ke kan gudanar da taro domin zaben wanda zai maye gurbinsa.

Mullah Akhtar Mansour, shugaban Taliban da Amurka ta kashe
Mullah Akhtar Mansour, shugaban Taliban da Amurka ta kashe 路透社照片
Talla

A jiya Asabar ne jirgin ya kaddamar da farmaki kan motar da ke dauke da marigayin a kan iyakar Afghanistan kuma mutuwarsa ta haifar da cikas ga kungiyar wadda ta kara karfafa a karkashin jagorancin Akhtar.

Tuni dai sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce, marigayin ya dade ya na haifar da barazana ga Amurka.

A watan Yulin bara ne, Mullah Akhtar ya maye gurbin Mullah Omar, wanda ya asassa kungiyar ta Taliban.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.