Isa ga babban shafi
Pakistan-Afghanistan

An Kashe Jagoran Taliban Mullah Akhtar Mansour

Hukumomi a kasar Afghanistan na nazarin yadda zata kasance bayan sanarwan  mutuwar jagoran Taliban dake kasar Mullah Akhtar Mansour wanda jiragen saman yakin Amurka da babu kowa ciki suka kashe.  

Jagoran kungiyar Taliban  Akhtar Mohammad Mansour wanda aka kashe
Jagoran kungiyar Taliban Akhtar Mohammad Mansour wanda aka kashe REUTERS/Taliban Handout
Talla

Ita dai kungiyar Taliban bata ce komi ba game da wannan ikirarin kashe mata shugaba.

Majiyoyin samun labarai a Amurka na cewa jiragen yakin Amurkan sun rutsa da Shugaban Taliban din ne a yankin Balochistan na kasar Pakistan dake kan iyakan Pakistan da Afghanistan.

Mai Magana da yawun Amurka Peter Cook ya fadi cewa mamacin na da hannu wajen ayyukan ta'addanci da kungiyar Taliban ke kaiwa a sassan yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.