MDD za ta sake zaman sasanta rikicin Syria
Jakaadan majalisar dinkin duniya kan sasanta rikicin Syria, Staffan de Mistura ya ce, zai sake gudanar da wani taron zaman lafiya a watan gobe bayan ya bukaci tsagaita wuta sakamakon sabon tahin hankalin da aka samu wanda ya hallaka fararen hula sama da 20 a birnin Aleppo.
Wallafawa ranar:
De Mistura ya bukaci kasashen Amurka da Rasha da su gaggauta tsoma baki a matakin kololuwa domin ceto tattaunawar zaman lafiyar kasar ta Syria.
A lokacin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan ya gana da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, Mr. De Mistura ya ce, yarjejeniyar da aka cimma a watan Fabarairu na cikin wani hali.
Wata kungiyar sa- kai doimin kare fararen hula, White Helmets ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, kananan yara na cikin wadanda suka mutu a sabon tashin hankalin wanda aka samu a jiya Laraba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu