An kai mummunan hari a Aleppo
Akalla mutane 25 aka kashe sakamakon ruwan wutar da aka yi wa yankin Aleppo a kasar Syria a ci gaba da tashin hankalin da ake samu a kasar, duk da shirin tsagaita wutar da ake aiwatarwa.
Wallafawa ranar:
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bayyana takaicinsa da barkewar sabon fadan, inda ya bukaci bangarorin da ke kai hare hare da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta.
Ban yace barkewar sabon fadar zai yi tarnaki ga shirin aikin jinkai da ake gudanarwa yanzu haka.
Yau ake sa ran Jakadan Majalisar Steffan de Mistura zai gabatar da rahotan cigaban da aka samu ga Kwamitin Sulhu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu