Isa ga babban shafi
MDD

MDD ta sauya tsarin daukan sakatarenta

Majalisar dinkin duniya ta saurari ‘yan takarar da ke neman maye gurbin sakatare janar na majalisar, Ban Ki-Moon wanda zai sauka daga mukaminsa a ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa, kuma a karon farko kenan da ta yi haka a bainal jama’a, abinda ya banbanta da tsarin da aka shafe shekaru 70 akai, inda wasu mambobinta guda biyar ke zaben wanda zai rike mukamin a sirce.

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon zai sauka daga kujerarsa a ranar 31 ga wata Disamba mai zuwa
Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon zai sauka daga kujerarsa a ranar 31 ga wata Disamba mai zuwa Reuters
Talla

Tun a ranar Talatar da ta gabata ne ‘yan takarar kujerar suka fara bayyana a gaban zauren majalisar dinkin duniya, inda suka sha tambayoyi akan batutuwa da dama da suka hada da rikice rikicen da duniya ke fama da su da kuma matsalar dimamar yanayi har ma da yakin gabas ta tsakiya.

Wannan sabon tsarin dai ya banbanta da wanda aka saba gani a baya, inda majalisar  ke yin tambayoyi a sirce ga wanda ke sha’awar darewa babban mukamin na jakadan duniya.

A can baya dai, batun daukan sakatare janar na hannun kwamitin tsaron majalisar ne da kuma mambobinta masu kujerun din-din-din da suka hada da Faransa da Birtaniya da China da Rasha da Amurka.

A yanzu dai, an bai wa dukkanin mambobi 193 damar shiga a dama da su wajen daukan sakatare janar din.

To sai dai duk da haka, kwamitin tsaron ne ke da alhakin yanke hukuncin karshe dangane da wanda za a dauka.

Amma dai a cewar shuganan majaliasar dinkin duniya Morgen Lykketoft , matukar dai kasashe da dama suka nuna goyon baynasu ga wani dan takara guda, babu dalilin da zai sa kwamitin ya so da wani abu daban da ya ban banta da ra’ayoyin sauran kasashen.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.