Isa ga babban shafi
Saudi-Egypt

Saudiyya Zata Gina Gada Bisa Teku Da Ya Hada ta Da Masar

Sarki Salman na kasar Saudiyya ya sanar da shirin samar da gada da zata ratsa kasar Masar zuwa Saudiyya, a wani alamari da ake ganin nuna goyon bayan ne karara ga shugaban Masar Abdel Fatah Alsisi.

Shugaban Masar  Abdel Fattah al-Sisi  ta hagu tare da Sarki Salman na Saudiyya a lokacin da Sarkin ya sauka a birnin Cairo.
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ta hagu tare da Sarki Salman na Saudiyya a lokacin da Sarkin ya sauka a birnin Cairo. REUTERS/The Egyptian Presidency/Handout via Reuters
Talla

Sarkin Saudiyya Salman mai shekaru 80 ya sanar da wannan aiki ne yayin wata ziyara ta kwanaki 5 da ya fara a kasar Masar.

Kasar Saudiyya dai ta kasance a sahun gaba na kasashen dake goyon bayan kasar Masar

 

Sarki Salman ya sanar da fara aikin ne bayan ya gana da Shugaban Masar a fadar sa Ittahidiya dake Cairo.

Dubban 'yan kasar Saudiyya ke tafiya Masar yawon shakatawa, haka nan kuma dubban 'yan kasar Masar ke tafiya Saudiyya aikin Hajji da Umra duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.