Ministan shari’ar Masar Ahmed al-Zind ya shiga tsaka mai wuya
Yanzu haka ministan shari’ar kasar Masar Ahmed al-Zind ya shiga tsaka mai wuya sakamakon kalaman da ya yi wanda al’ummar Musulmin kasar ke kallon sa a matsayin cin zarafin Manzan Allah (SAW).
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tuni Gwamnatin Masar ta kori Ministan shari’ar kasar saboda katobarar da yayi na cewar ko Manzan Allah wanda tsira da amincin Allah suka tabbata a gare shi ne yayi masa kazafi zai sa a kama shi a hira sa da tashar talabijin din Sada al Balad.
Ministan yayi katobarar ce wajen mayar da martani kan kama wani Dan Jarida saboda zargin cewar ya bata masa suna.Sai dai kafin kammala shirin, ministan ya nemi ahuwa, inda ya ce subutar baki ne, amma hakan bai sa ya tsira ba daga suka daga dubban mutane.
Ita ma Jami’ar Al Azhar ta yi gargadi a kai, inda ta bukaci mutunta Manzan Allah (SAW), yayin da kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights watch ta ce irin wadannan kalamai na haifar da tashin hankali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu