Isa ga babban shafi
Masar

An kame wasu shugabannin adawa da Mubarak a Masar

Hukumomin Kasar Masar sun kama wasu shugabannin matasa 4 da suka jagoranci juyin juya halin da ya yi sanadin kawo karshen gwammnatin Hosni Mubarak a 2011. Wata Majiyar shari’ar kasar tace kama shugabannin na zuwa ne kasa da wata guda kafin cika shekara 5 da juyin juya halin da ya kawar da Mubarak daga karagar mulki.

Tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak
Tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak REUTERS/Stringer/Files
Talla

Shugabannin sun hada da Sherif Arubi da Mohammed Nabiol da Ayman Abdel Megid da Mahmud Hesham inda ake tuhumarsu da tinzira jama’a.

Za a ci gaba da tsare mutanen hudu har na tsawon kwanaki 15.

Tun kawar da gwamnatin Muhammed Morsi a 2013, mahakuntan Masar ke murkushe ‘Yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.