Isa ga babban shafi
Masar

Yan sandan Masar na kamen dalibai yan Najeriya

‘Yan sandan Masar na kamen Dalibai galibinsu ‘Yan Najeriya a yayin da suke gudanar da harakokinsu na yau da kullum a Makaranta ko wajen cinikayya, kawo yanzu dai babu wani dalili da ya kai ga yin kamen Daliban

Yan sanda a Masar
Yan sanda a Masar REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

Ana ganin cewa kamen na yau laraba baya rasa nasaba da mataki dama yunkurin mahukuntan kasar ta Masar na fitar da masu tsatsauran ra’ayi a cikin kasar.

sakamakon yadda kasar ke ci gaba da fuskantar barazanar tsaro daga kungiyar ISIL mai da’awar Jihadi ganin yadda take kaiwa baki masu yawon bude ido a kasar hari.

A bara Masar ta fuskanci munanan hare haren ta’addanci akan baki da suka shigo kasar musanman kakkabo jirgin saman kasar Rasha da kungiyar ISIL ta dauki alhakin kaiwa, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar Rashawa  sama da 200.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.