Burundi
Komitin Sulhu na MDD ya Umarci tura 'Yan Sanda Burundi
Komitin Sulhu na MDD ya umarci Babban Sakatare Janar na Majalisar Ban Kimoon da ya gaggauta tura ‘yan sanda zuwa kasar Burundi, inda ake fargaban kazancewa rikicin kabilanci a fadin kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Shekara daya kenan ake samun kashe-kashen mutane a kasar tun lokacin da Shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya kafe da sai ya zarce da mulki bayan cikan waadin mulkin sa kamar yadda kundin tsarin mulki ya nema.
Rayukan mutane 439 suka salwanta ya zuwa yanzu, yayinda wasu mutane dubu 250 aka tilasta masu tserewa daga gidajensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu