Isa ga babban shafi
Faransa

Fasinjar jirgin sama ta boye yarinya a cikin jaka

Wata mata da ta shiga jirgin saman Air France daga kasar Turkiya zuwa birnin Paris na hannun jami’an tsaro saboda boye wata ‘yarta mai shekaru hudu cikin jaka don kada ta biya ma ta kudin shiga jirgin saman.

Jirgin Air France
Jirgin Air France Spaceaero2/Wikimedia.org
Talla

Wannan mata dai wadda aka sakaya sunanta, ta shiga jirgin saman Air France ne daga birnin Santanbul na kasar Turkiya zuwa Paris na kasar Faransa, kuma dukkan bincike an yi ma ta kafin ta shiga jirgin saman.

Wasu majiyoyin sun ce, jami’an kwastan har sun dago cewa wata jaka da ke hannunta da mutun a ciki, lamarin da ya sa aka hana ta matsawa zuwa inda jirgin ya ke, amma kuma ta shammaci jami’an tsaron har ta shige cikin jirgin.

Bayan tashin jirgin ne, yarinyar ta nemi fitowa daga cikin jakar sakamakon murdawar ciki domin kewayawa bayan gida kamar yadda majiyoyi suka sanar, abinda ya sa asiri ya tonu.

Da saukansu a filin jiragen sama na Charles De Gualle da ke Paris aka tsare matar da ‘yar karamar yarinyar.

Wasu da suka san matar sun ce, ba ita ta haifi ‘yarinyar ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.