Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ba za ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba

Kasar Faransa ba za ta taba amincewa da kafuwar cikakkiyar kasar Falasdinu ba, idan Falasdinawan ba su amince da sake farfado da tattaunawar samar da zaman lafiya tsakaninsu da kasar Isra'ila ba.

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Marc Ayrault.
Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Marc Ayrault. REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Fransa Jean-Marc Ayrault ne a jiya laraba a birnin Al-Kahira na kasar Masar ya bayyana daukar wannan mataki, idan aka samu akasin abinda kasar ta bukata daga Falasdinawa.

Wannan dai ya yi hannun riga da matsayin da magabacinsa Laurent Fabius ya dauka a karshen watan janairun da ya gabata, wanda ya haifar da matukar bacin rai ga gwamnatin yahudun Isra'ila sakamakon shawarar shirya gudanar da wani taron kasashen duniya domin sake farfado da tattaunawar neman zaman lafiya tsakanin Yahudawa da Falasdinawa da ke ci gaba da tafiyar hawainiya.

Ministan harkokin wajen na Fransa na wancan lokacin, Laurent Fabius ya gargadi Isra'ila da cewa,matukar aka samu kuskure daga bangarenta, to kuwa nan take Faransa za ta amince da Falasdinu a matsayin cikakkiyar kasa mai cikkaken 'yanci.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.