Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton da Trump sun samu nasara

Hillary Clinton ‘Yar takarar neman shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrates da Donald Trump na Republican, sun yi nasara a zaben fitar da gwani da aka yi a cikin daren jiya, a mafi yawa daga cikin jihohi 12 na kasar.

Hillary Clinton ta Demorat da Donald Trump na Republican
Hillary Clinton ta Demorat da Donald Trump na Republican REUTERS/David Becker/Nancy Wiechec/Files
Talla

Clinton ta samu nasara a Jihohin Amurka 7 cikin 11 inda ta doke babban mai hammaya da ita Berni Sandars a Jihohin kudancin Amurka da suka hada da Alabama da Arkansas da Georgia da Tennessee da Texas.

Sannan ta lashe zaben a Massachusetts.

Sanders ya samu nasara a jihohin Vermont da Oklahoma da Colorado da kuma Minnesota.

Trump ya lashe Jihohi 7 cikin 11 a bangaren zaben fitar da gwanin na Jam’iyyar Republican.

Trump ya samu nasara akan babban mai hammaya da shi Ted Cruz wanda ya zo a matsayi na biyu.

Sakamakon zaben na ranar Talata ya nuna Hillary Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican zasu kasacne ‘yan takarar jam’iyun biyu a zaben shugaban kasa.

Wani sakamakon jin ra’ayin jama’a da kafar talabijin ta CNN ta gudanar, ya nuna Clinton ta doke Trump.

Masu sharhi na ganin rabuwar kai tsakanin ‘Yan takarar Republican nasara ce ga Democrat. Masana siyasar Amurka na ganin Clinton zata samu nasara a zaben Amurka da za a gudanar a watan Nuwamba idan dai har aka tsayar da Trump a matsayin dan takarar Republican.

01:31

Clinton da Trump sun samu nasara a Zaben fitar da gwani a Amurka

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.