Isa ga babban shafi
EU

Shirin dakile hanyoyin tallafawa 'yan ta'adda a duniya

Kungiyar tarayyar Turai ta fitar da wasu shirye-shiryen dakile duk kafofin da ake tallafawa ‘yan ta’adda da kudade a duniya, a dai dai lokacin da Faransa ke zafafa yaki da ta’addanci.

Ana zargin wasu kasashe da tallafawa 'yan ta'adda  a duniya
Ana zargin wasu kasashe da tallafawa 'yan ta'adda a duniya © AP
Talla

Kungiyar da ke da mambobin kasashe 28, ta fitar da tsare tsaren ne bayan kammala zaman majalisarta a birnin Strasburg na Faransa.

Daga cikin shirin akwai bin diddigin asusun ajiyar kudade a kasashen da ake zargin cewa ‘yan ta’adda na samun mafaka ko kuma kasashen da ake zargin suna tallafawa ‘yan ta’addan.
 

A makon jiya ne Faransa ta soki kungiyar tarayyar Turai game da jan kafar da ta ke yi wajen daukar matakan farautar ‘yan ta’addan.

A cewar tarayyar Turai, daga cikin tsare tsaren har da nakasa hanyoyin samun kudaden shigar kungiyoyin da ya hada da na kungiyar IS.

Yawaitar hare haren ta’addanci a nahiyar ne dai ya sanya kungiyar tashi tsaye da nufin magance matsalar.

A makon gobe ne ake sa ran kungiyar za ta mika wa ministocin nahiyar Turai taftarin wannan bukatar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.