Isa ga babban shafi
EU-AFRIKA

Turai za ta horar da Afrika a kan yaki da Ta’addanci

Kungiyar kasashen Turai za ta kaddamar da wani Sabon shirin bada horo na musamman a yankuna gabashin Afrika, domin taimkawa hukumomin tsaro wajen aiwatar da bincike a kan Iyakokin kasashensu da kuma hanyar hukunta masu laifufuka, lura da yadda ayyukan Jihadi ke cigaba da ta’azara a yankuna.

Wasu daga cikin wakilan Kungiyar Kasashen Turai
Wasu daga cikin wakilan Kungiyar Kasashen Turai REUTERS/Vincent Kessle
Talla

Kungiyar kasashen turai na shirin kadamar da Sabon shirin ne a farkon shekarar 2016, a kasashen Kenya, da Ethiopia da Eritrea da Djibouti da sudan ta kudu da sudan da Uganda da kuma kasar Yemen, shirin da kungiyar ta ce za ta kashe sama da euro miliyan 11 a cikin shekaru 5.

Uwe Wissenbach shugaban sashen siyasa a kungiyar a Kenya, ya ce shirin, zai fi mayar da hankali wajen horor da kanana hukumomin dokoki da shari'a akan hanyoyin bincike laifukan ta’adanci.

Sanar da Wannan shiri na zuwa ne adai-dai lokacin da kungiyar ke shirin gudanar da taro na musamman a birnin Nairobi akan tunkara matsalar ta ‘adanci da tsaro a Afrika.

Masana dai na cigaba da cewa, cin hanci tsakanin Jami’an tsaro na daya daga cikin abubuwa da ke cigaba da haifar da yaduwar ta’adanci da rashin tsaro a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.