Cutar Zika ta shiga Denmark
Hukumomin kiwon lafiya a kasar Denmark sun ce yanzu haka an kwantar da mutun na farko da ake zargin cewa yana dauke da kwayar cutar Zika, wadda ke ci gaba da yaduwa a cikin kasashen Latin Amurka.
Wallafawa ranar:
An dai kwantar da mutumin ne da aka ce bai jima da dawowa daga wata kasa ta kudancin Amurka ba, inda ake fargabar ya kamu da wannan cuta ta Zika, wadda ke sa ana haifar yara da kananan kawuna.
Ita ma Birtaniya ta ce, matafiyanta da ke dawowa daga yankin kudancin Amurka, sun shigo da cutar yayin da kasar Netherlands ta tabbatar cewa 'yan kasarta 10 na dauke da cutar bayan sun dawo daga yankin kudancin Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu