Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta kashe sojoji a harin Kandahar

Akalla sojoji 22 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da kungiyar Taliban ta kaddamar a filin jiragen sama na Kandahar da ke yankin kudancin Afghanistan.

Mayakan kungiyar Taliban
Mayakan kungiyar Taliban REUTERS
Talla

Kungiyar Taliban ta rasa mayakanta 9 a farmakin wanda ta kai a cikin daren jiya akan gine-ginen da ke dauke da ma’aikatan gwamnati da jami’an sojin Afghanistan da na Amurka da na kungiyar tsaro ta NATO.

Mayakan Taliban sun labe a cikin gine-ginen, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin iyalan sojojin da suka hada da mata da kananan yara .

Tuni dai aka tura sojoji na musamman zuwa filin jiragen saman kuma suna ci gaba da aiki da nufin karbe filin daga hannun Taliban.

Rahotanni sun ce mayakan Taliban sun yi amfani da bindigogi kirar AK-47 yayin da suka sanya kakin soji a fafatawar da suka yi na tsawon sa’oi da sojojin.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugabannin yankin ke gudanar da taro a Pakistan da nufin tattaunawa kan rikicin kasar Afghanistan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.