Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

An bukaci Paparoma ya kare martabar asusun bankin Vatican

Shugaban mabiya darikar Katholika a duniya Paparoma Francis zai ci gaba da aikin samar da sauye sauye a majami’un Katholika duk da badakalar cin hanci da rashawa da ta kunno kai a fadar Vatican wadda kuma ke a matsayin barazana game da aikinsa.

Shugaban darikar Katholika Paparoma Francisco
Shugaban darikar Katholika Paparoma Francisco REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

Shugaban ma’aikatan Paparoma Francis, Giovanni Angelo Becau ya bayyana cewa ya gana da Paparoman, inda ya ce kalamansa na nuna cewa a shirye ya ke ya ci gaba da kokari wajan tabbatar da sauye sauye a Majami’un Katolika duk da wannan badakalar da ta kunno kai.

Shi kuwa Nunzio Galantino shugaban kungiyar masu mukamin Bishop a Italiya ya shaidawa kafar talabijin ta 2000 cewa, yanzu haka Paparoman na cikin damuwa game da wannann batu na dakalar cin hanci da ta yi sanadiyar kama wasu mutane biyu da ake zargin da leken asiri.

Inda suka fallasa wata takarda ga manema labarai wadda ke dauke da bayanai kan yadda aka kashe kudaden fadar Vatican ba bisa ka’ida da ya hada da yadda aka yi amfani da kudaden assusn taikama wa marasa galiho wajen kawata gidajen manyan limaman na Vatican.

Mukarraban Paparoman dai sun buka ce shi da ya yi amfani da karfin ikonsa wajan kare martabar asusun bankin Vatican, to sai dai bisa dukkan alamu sabon badalakar za ta rura wutar caccakar da a ke yi dangane da shirinsa na samar da sauye sauyen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.