SYRIA
'Yan gudun hijra: EU za ta bai wa Jordan tallafi
Kungiyar tarayyar Turai ta bayyana cewa za ta bai wa kasar Jordan tallafin Euro miliyan 28 domin kula da ‘Yan gudun hijirar Syria da ke samun mafaka a kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Kwamishinan kula da jin dadin jama’a na kungiyar ne Christos Stylianides ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara a sansanin Zaatari da ke yankin Arewacin Jordan, inda ‘yan gudun hijira dubu 80 ke samun mafaka.
Ana sa ran za a yi amfani da wadannan kudaden wajan kula da lafiyar ‘yan gudun hijirar da kuma samar musu da tsaftataccen ruwan sha har ma da ba su ilimi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu