Isa ga babban shafi
CANADA

Jam'iyyar Liberal a Canada ta lashe zabe

Jam'iyyar Liberal a kasar Canada ta lashe zaben kasar abinda ya kawo karshen shekaru  9 da jam'iyyar Conservative ta masu ra'ayin rikau wadda Firaminista Stephen Harper ke jagoranta.  

Justin Trudeau na jam'iyyar Liberal dake kasar Canada
Justin Trudeau na jam'iyyar Liberal dake kasar Canada REUTERS/Chris Wattie
Talla

Sakamakon zaben ya nuna cewa jam'iyyar Liberal dake karkashin jagorancin Justin Trudeau na kan gaba a mazabu 185 yayin da Jam'iyyar Conservative ta Harper keda mazabu 103.

Tuni Harper ya amsa shan kaye,ya kuma taya Trudea murna da kuma sauka daga  jagorancin jam'iyyar su,yayin da Trudeau wanda mahaifin sa ya taba jagorancin kasar a matsayin  Firaminista yayi jawabin murna da kuma kama hanyar kafa sabuwar Gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.