Isa ga babban shafi
Faransa

Syria: Faransa ba za ta kyamaci 'Yan gudun hijira Musulmi ba

Gwamnatin Faransa ta bayyana adawarta da bukatar wasu Magadan garin kasar wadanda suka ce ‘Yan gudun Hijira Kiristoci ne kawai zasu karba a biranensu. Wannan kuma na zuwa ne bayan Faransa ta ce zata karbi ‘Yan gudun hijirar Syria kimanin 24,000 a cikin shekaru biyu.

Ministan cikin gidan Faransa, Benard Cazeneuve
Ministan cikin gidan Faransa, Benard Cazeneuve REUTERS/Regis Duvignau
Talla

Ministan cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve ya yi allawadai da wasu Magadan garin kasar, da suka ce ‘Yan gudun Hijira Kiristoci ne kawai za su karba a biranensu.

Ministan ya ce Faransa za ta karbi ‘Yan gudun hijirar ba tare da nuna banbanci ba tsakanin Musulmi da Kirista.

Ministan ya shaidawa kafar talibijin din Faransa cewa rikicin Syria ya shafi Musulmi da Kirista, domin kowa kashewa ake yi kasar. A cewarsa Faransa za ta karbi kowa ba tare da nuna banbancin addini ba.

Magajin garin Roanne Yves Nicolin da na Belfort a gabacin Faransa ne suka ce kiristoci ne kawai zasu karba wadanda mayakan IS ke kashewa saboda addininsu.

Wannan kuma na zuwa ne bayan Faransa tace za ta karbi ‘Yan gudun hijirar Syria kimanin 24,000 cikin shekaru biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.