Isa ga babban shafi
China

Ana fargaba kan faduwar hannayen Jari

Masana tattalin arziki sun fara bayyana fargabar su kan faduwar hannayen jari a kasashen duniya, wanda shi ne irinsa na farko da aka taba samu tun shekarar 2008.

'Yan kasuwa sun shiga damuwa a China sakamakon faduwar hannayen jari
'Yan kasuwa sun shiga damuwa a China sakamakon faduwar hannayen jari REUTERS/China Daily
Talla

Duk da ya ke masana na cewar lokaci bai yi ba da mutane za su yi fargabar komawa irin yanayin da aka shiga a shekarun 1997 da 2008, amma idan aka ci gaba da samun yadda hannayen jarin ke faduwa ‘yan kasuwa za su shiga hali na rashin tabbas.

Faduwar kashi Takwas da rabi da aka samu a China jiya, ya sa daukacin kasuwannin hannayen jarin duniya sun samu makasu a hada-hadarsu ta ranar Litinin, yayin a yau Talata aka sake samun irin wannan matsalar a China da Argentina.

Wannan dai na faruwa ne sakamakon koma-bayan da kasuwannin hannayen jari na kasar China, lamarin da ke barazana ga tattalin arzikin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.