Isa ga babban shafi
EU

Tsarin haraji ga hannayen Jari a Turai

Ministocin kudin kasashen nahiyar Turai sun amince da sabon tsarin haraji ga kasuwannin hannayen jari wanda za'a kaddamar a 2016 duk da Birtaniya na adawa da tsarin. Wannan kuma matakai ne da kasashen ke dauka domin farfado da kasuwar hannayen jarin da suka fuskanci matsaloli tun a 2008.

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai Herman Van Rompuy
Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai Herman Van Rompuy Reuters
Talla

Faransa da Jamus da suka jagoranci tabbatar da tsarin sun ce zasu bi tsarin daki-daki har a samu biyan bukata, amma Birtaniya tana ganin tsarin zai janyo wa kasuwanninta matsala, tare da fargabar masu saka jari zasu iya ficewa kasar don gudun kada su biya kudaden harajin.

Akan Haka Birtaniya ta sha alwashin zata kalubalanci tsarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.