Isa ga babban shafi
Ukraine

Majinyatan cutar Sida na cikin hatsari a Ukraine

Hukumar yaki da cutar Sida ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci taimako na samar da magunguna ga al’ummar gabashin Ukraine dubu takwas da ke fama da cutar sakamakon karancin magani, domin ba su damar ci gaba da rayuwa.

Maganin Cutar Sida
Maganin Cutar Sida AFP PHOTO / ADEK BERRY
Talla

Wakilin hukumar da ke yaki da cutar kanjamau ta Majalisart Dinkin Duniya Mr Michael Kazatchkin ya sanar cewa karancin magungunan da masu dauke da cutar ke fuskanta babban barazana ce ga rayuwar su yana mai cewa akwai bukatar gaggauta kawo dauki ga al’ummar da ke cikin tsaka mai wuya sakamakon rikici tsakanin Ukraine da bangaren ‘Yan aware na Rasha.

Mr Kazachtkine ya yi kira ga kasashen Amurka da Jamus da Faransa da Ukraine da Rasha da su dauki matakin gagguta kai dauki ga majinyatan domin kaucewa bala’in da za su fada idan har maganinsu ya kare.

Mutanen dubu takwas da ke fuskantar wannnan matsalar na zaune ne a yankin Lugansk da Donesk da Rasha ke kokarin ganin sun balle daga kasar ta Ukraine.

Yankin dai ya kasance matattarar kashi 25 cikin dari na wadanda ke dauke da cutar Sida a kasar Ukraine sai dai yawancin su yanzu sun tsere sakamakon yaki a kasar.

Ukraine dai ta hana shiga da magungunan da wasu allurai da ake yi wa masu cutar ta Sida saboda ana bukatar rakiyar sojoji wajen shigar da magungunan wanda ya kasance babban barazana a halin da ake ciki a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.