Kerry ya sami sauki daga karaya
Bayan da aka sallame shi daga asibiti, inda yayi jinya kafar daya karye, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace nan bada dadewa ba zai nufi birnin Viennan kasar Autria, inda za a ci gaba da tattauna batun Nukiliyan kasar Iran.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yayin da wa’adin yarjejeniyar ke karatowa, Kerry, dake tafiya da sanda a lokacin da yake barin babban Asibitin birnin Boston ya shaiwa manema labaru cewa zai shiga a dama dashi a yajejeniyar.
Ranar 31 ga Watan Mayun da ya gabata Kerry mai shekaru 71 a duniya ya karya kafa, lokacin da yake tuka keke a tsaunkan Kasar Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu