Colombia za ta kaddamar da hari akan ‘Yan tawayen FARC
Shugaban Kasar Colombia Juan Manuel Santos ya bai wa sojojin kasar umurnin kaddamar da sabbin hare hare kan ‘Yan Tawayen FARC bayan sun kashe sojoji 10 a wani harin kwantar baunar da suka kai mu su. A jawabin da ya yi wa al’ummar kasar ta talabijin shugaba Santos ya ce za a ci gaba da kai hare haren har illa masha Allahu.
Wallafawa ranar:
A baya dai an dakatar da fafatawar ne na wata guda bayan da ‘yan Tawayen suka amince da tsagaita wuta a shirin zaman lafiyar kasar a Havana.
‘Yan tawayen sun kai harin ne a yammacin Colombia kuma shi ne hari mafi muni da aka kai bayan kaddamar da shirin amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu