Isa ga babban shafi
Amurka-Isra'ila

Obama: Babu wani sabon abu a jawabin Netanyahu

Shugaba Barack Obama ya ce babu wani sabon batu da Firaminstan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gabatar a jawabin da ya yi a zauren majalisar Amurka. Yayin da ya ke mayar da martini kan jawabin, Obama ya ce Netanyahu bai gabatar da wani shirin da ya fi inganci kan yadda za a magance matsalar kasar Iran ba.

Shugaban Amurka, Barack Obama.
Shugaban Amurka, Barack Obama. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A jawabinsa, Netanyahu ya ce Iran makiyar Amurka ce. Kuma a cewarsa tattaunawar da manyan kasashen duniya ke yi da Iran dama ce na budewa kasar kofar mallakar makaman nukiliya sabanin kokarin dakile kudirin na Iran.

Netanyahu ya shaidawa Majalisar Amurka cewar ko da sunan wasa Isra’ila ba zat a bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, yana mai cewa idan duniya ta kawar da kai, Isra'ila ita kadai na iya daukan matakai.

Netanyahu ya ce ya san Amurka ba za ta juya wa Isra’ila baya ba.

Tuni dai Iran ta yi watsi da kalaman Netanyahu akan batun yarjejeniyar nukiliya tsakaninta da manyan kasashen Yammacin duniya.

Obama ya bayyana fatar sa na ganin an samu nasara a tattaunawar da suke da kasar Iran, amma Netanyahu ya bukaci Majalisar Amurka ta dakile duk wani yunkuri na sasantawa da Iran.

Rahotanni sun ce bangaren Jam'iyyar Republican mai adawa ne suka gayyaci Netanyahu ba tare da sanin fadar White House ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.