Isa ga babban shafi
Ukraine

Amurka ta jinkirta shirin ba Ukraine Makamai

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya amince ya jinkirta shirin bai wa kasar Ukraine makamai don yaki da ‘yan tawayen kasar da ke samun goyan bayan Rasha kamar yadda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukata. Obama ya amince ya jinkirta shirin ne bayan ya gana da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Angela Merkel da Barack Obama
Angela Merkel da Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Merkel tace matakin zai bayar da damar tattaunawar diflomasiya da shugaba Vladimir Putin don kawo karshen matsalar da ake samu a kasar.

Obama ya bayyana fatar Shugabar gwamnatin Jamus za ta cim ma yarjejeniya da shugaban Rasha domin kawo karshen rikicin Ukraine da aka shafe tsawon watanni 10 ana zubar da jini a gabacin kasar.

A gobe Laraba ne ake sa ran Shugabannin Jamus da Faransa za su jagoranci tattaunawar sulhu tsakanin Shugaban Ukraine Petro Poroshenko tare da Shugaban Rasha Vladimir Putin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.