Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

An ki amincewa da bukatar Falasdinawa

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ki amincewa da bukatar Falasdinawa na samun ‘yanci domin kawo karshen mamayar da Isra’ila ta yi wa yankunansu cikin shekaru uku. Amurka da Australia sun hau kujerar na-ki yayin da kasashe biyar ciki har da Birtaniya suka kaurace.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, a zauren Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, a zauren Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Mike Segar
Talla

Kasar Jordan ce ta gabatar da kudirin a kwamitin sulhu don ganin an samu dawwamammen zaman lafiya a Yankin Gabas ta Tsakiya.

Kasashen da suka goyi bayan kudirin sun hada da Rasha da China da Faransa da Argentina da Chadi da Chile da Jordan da kuma Luxembourg.

Kasashen Amurka da Australia sun ki amincewa da bukatar yayin da kasashen Birtaniya da Lithuania da Najeriya da Koriya ta Kudu da Rwanda suka ki kada kuri'a.

Kudirin ya gaza samun kuri’u 9 daga cikin kujeru 15 na kwamitin.

Kudirin ya kunshi wa’adin watanni 12 ga Isra’ila ta gaggauta amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya tare da ficewa yankunan Falasdinawa da ta mamaye kafin karshen 2017.

Bayan kin amincewa da kudirin a kwamitin sulhu, Kasar Isra’ila ta bayyana jin dadinta, tana mai cewa kin amincewa da matakin shi ne kawai hanyar samar da zaman lafiya a Gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.