Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar dunkin Duniya ta yi kashedi kan yaduwar makamai a yankin Sahel

Majalisar dinkin duniya ta bayyana dari dari dangane da yadda yan kungiyar IS ke kara karfi a kasar Libya, al-amarin daya sa ta bayyana cewa, yake-yaken da ‘yan kungiyar ke kaddamarwa a kasar, na barazanar da ta shafi kasashen yankin Sahel.

newint.org
Talla

Majalisar Dinkin duniyar ta kara da cewa, ya zama wajibi a dau matakin magance wannan al-amarin da gaggawa kafin ya tsananta, domin fadan da mayakan jihadi ke yi na matukar barazana ga kasashen yankin na Sahel.

Jakadan Majalisar dunkin Duniya a yankin Sahel ya ce muddin ba’a yi gaggawar magance matsalar a kasar Libya ba, nan gaba mayakan na jihadi za su tarwatsa daukacin kasashen yankin.

Kasar Libya dai ta fada cikin tashin hankali ne, tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Mu’ammar Gaddafi, inda ko a baya-bayan nan ‘yan tawaye sun afkawa Majalisar kasar da miyagun makamai, duk da kokarin da Dakarun Majalisar dunkin Duniya ke yi na kai karshen tashin hankalin.

Yanzu haka dai babbar barazanar da ake huskanta ita ce yadda aka lura da kwararar akalla makamai 20,000 zuwa kasashen na Sahel daga kasar ta Libya, bayan kammala juyin juya halin kasar.

Baya ga wannan kuma an ce masu sumogal, sun shigar da akalla tone 18 na Hodar Ibilis.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.