Isa ga babban shafi
China-Amurka

China da Amurka sun amince da rage dumamar yanayi

Fadar White House ta Amurka ta bayyana cewar China da Amurka sun amince da kulla hasashen samar da shirin rage dimamar yanayi, a yayin da kasar ta China ta shirya soma aiwatar da shirin, ya zuwa shekarar 2030

Barack Obama da Xi Jinping na China
Barack Obama da Xi Jinping na China REUTERS/Kim Kyung-Hoon
Talla

Wannan dai shi ne karon farko da aka samu kasar ta China wadda ta fi kowace kasa a Duniya yawan al’umma ta shata wa’adin soma aiwatar da shirin rage dimamar yanayi kuma a cikin hanzari.

A dayan gefen kuma kasar Amurka ta bayyana nata shirin rage dumamar yanayin da kashi 26 zwa 28 daga shekarar 2005 nan da 2025.

Wannan batun dai ya taso ne a yayin da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya hadu da na China Xi Jinping domin tattaunawa kan wannan batu a birnin Beijing.

Dama dai masana harkokin kimiyya sun tafka muhawarar cewar muddin ana bukatar rage dimamar yanayi a Duniya domin cimma hasashen Majalisar dunkin Duniya na tsaida yanayin Duniyar akan kashi 4 na ma’aunin Celsius , to dole ne a dauki mataki na rage yadda Masana’antu ke samar da hayaki mai turnuke sararin samaniya.

Kasashen China da Amurka kadai na samar da kashi 45 na Carbon Dioxide, Hayakin da ke raggwanta yanayin sararin samaniya.

An dai yi ittifakin cewar wannan matsalar ce ke haddasa Fari, da ambaliyar Ruwa, da kuma bushewar wurare masu dausayi a ban Kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.