Isa ga babban shafi
Amurka-Iraqi

Iraqi: Amurka ta yi kokarin kubutar da Foley

Kasar Amurka tace ta yi kokarin ceto Amurkawan da aka yi garkuwa da su a Syria cikin su har da da Dan Jarida James Foley da Mayakan IS suka kashe amma yunkurin bai yi nasara ba. ma’aikatar tsaron Amurka, tace ta tura Sojoji domin kubutar da ‘Yan kasar.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Kakakin Ma’aikatar tsaron Amurka Admiral John Kirby yace Amurka ta tura sojojin sama da kasa cikin Syria don kubutar da mutanen da ke hannun kungiyar ISIS amma hakarsu ba ta cim ma ruwa ba, domin an kwashe wadanda ake garkuwa da su inda suka kai samamen.

Wannan ikirarin na Amurka na zuwa ne bayan Mayakan Iraqi da ke fafutukar kafa Daular Islama a kasar sun fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda suka kashe Dan Jarida James Foley tare da yin barazanar kashe na biyu muddin Amurka ba ta dakatar da kai harin sama a kasar ba.

Mayakan suna nuna Dan Jarida na biyu Steven Sotloff tare da cewar ransa na hannu Shugaba Barack Obama.

Kasar Amurka tace tana tunanin tura Karin sojoji 300 kasar Iraqi don karfafa tsaro a ofishin Jakadancinta. Wani jami’in gwamnatin Amurka yace bukatar hakan ta fito ne daga ma’aikatar harkokin wajen kasar don kaucewa irin matsalar da aka samu a kasar Libya inda aka kai harin da ya kashe babban Jami’in Diflomasiyar kasar a Benghazi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.