Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Amurka ta kakabawa Rasha sabbin takunkumi

Shugaba Barack Obama yace ya zama wajibi Amurka ta kakabawa kasar Rasha takunkumi saboda kazancewar rikicin Ukraine, yayin da masu kishin Rasha suka sake karbe ikon wani gari a gabacin kasar. Obama wanda ke ziyara a kasar Philippines yace sabbin takunkumin sun hada da haramtawa Rasha fitar da kayayyaki da suka kunshi na fasaha a wani mataki da ya ke ganin zai tursasawa shugaba Putin sauya ra’ayinsa ga rikicin Ukraine.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Kim Hong-Ji
Talla

A yau Litinin ne kuma Manyan Jami’an kasashen Turai zasu gana a Brussels inda ake sa ran zasu yi nazari akan sabbin takunkumin da zasu kakabawa kasar Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.