Isa ga babban shafi
Syria-Geneva

Gwamnatin Assad ta soki Amurka

Majalisar Dinkin Duniya ta kasa sasanta bangarorin da ke rikici a kasar Syria a zaman sasatawa da ake yi a Geneva inda wakilan gwamnatin Assad suka karkatar da alkiblar tattaunawar zuwa ga sukar Amurka.

Babban mai shiga tsakanin rikicin kasar Syria Lakhdar Brahimi
Babban mai shiga tsakanin rikicin kasar Syria Lakhdar Brahimi REUTERS/Denis Balibouse
Talla

A yau Laraba ne Lakhdar Brahimi babban mai shiga tsakanin rikicin Gwamnatin Syria da ‘Yan adawa zai ci gaba da jagorantar zaman tattaunawar bayan an dage zaman sasantawar a ranar Talata.

‘Yan adawa ne suka bukaci a dage ranar saboda babu haske da suke samu daga bangaren gwamnati game da batun shugabancin Syria.

A zaman taron, wakilan Gwamnatin Assad sun karkatar da batun shugabanci bayan sun dauko batun Amurka akan tana shirin mika makamai ga ‘Yan tawaye tare da zargin Amurka akan yin zagon kasa ga kokarin sasantawa.

Kamfanin Dillacin labaran Reuters ne ya ruwaito cewa majalisar kasar Amurka ta amince da bukatar a mika makamai ga ‘Yan adawa,

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.