Isa ga babban shafi
Masar-Saudi

Saudiya za ta tallafawa Masar idan Turawa sun janye Tallafinsu

Kasar Saudiya ta bukaci hadin kan kasashen Larabawa domin taimakawa kasar Masar idan har kasashen Turai sun janye Tallafinsu saboda adawa da yadda aka murkushe magoya bayan Mohammed Morsi.

Dubban Masu zanga-zanga a kasar Masar
Dubban Masu zanga-zanga a kasar Masar REUTERS/Beawiharta
Talla

Kamfanin Dillacin labaran Saudiya na SPA ya ruwaito Ministan harakokin wajen kasar Yarima Saud al-Faisal yana mayar da martani ga kasashen da suka yi gargadin za su janye Tallafin da suke ba Masar.

“Kasashen Larabawa da musulmi suna da arzikin da za su tallafawa kasar Masar”, a cewar Yarima Faisal.

Akwai wani taron gaggawa da ministocin harakokin wajen kasashen Turai za su gudanar a ranar Laraba domin tattauna makomar huldarsu da kasar Masar.

Tuni Shugabannin kungiyar Turai suka nemi mahukuntan Masar su gaggauta daukar matakan kawo karshen zubar da jinni a kasar.

Akwai Tallafin kudi na euro Biliyan 5 da kasashen Turai suka yi alkawalin ba kasar Masar, kuma tun a bara ne suka amince da tallafin.

Kasashen dukkaninsu sun yi Allah Waddai da yadda aka yi amfani da karfi wajen Murkushe magoya bayan Morsi da kuma harin da aka kai a Sinai wanda ya kashe ‘Yan sandan Masar 25 a kan iyakar kasar da Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.