Isa ga babban shafi
ICC

Kotun Duniya ta cika shekaru 15

A ranar 17 ga watan Yuli ne Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ke cika shekaru 15 da kafuwa wacce aka kafa domin hukunta laifukan yaki na bai daya a duniya. Wannan kuma na zuwa a dai dai lokacin da shugabannin kasashen Afrika ke zargin kotun ta fi mayar da hankali wajen farautarsu.

Fatou Bensouda Babbar mai gabatar kara a kotun ICC
Fatou Bensouda Babbar mai gabatar kara a kotun ICC AFP/Emmanuel Dunand
Talla

A shekarar 1998 ne kasashen duniya suka hadu a birnin Rome da ke kasar Italiya domin kafa wannan kotun.

Muradan Kotun su ne a samar da kotu ta bai daya a duniya da za ta hukunta aikata manyan laifuka da suka shafi cin zarafin bil Adama a duniya da kuma biyan diyya ga wadanda abin ya shafa.

A tashin farko, wasu da dama sun nuna cewa wannan ba batu ba ne mai yiwuwa, sai dai a wata rubutacciyar sanarwa da shugaban kotun Sang Hyung Song ya fitar, ya ce an shammaci mutane domin kotun ta tabbatar da tasirinta, yana mai cewa Kotun ta karbi kararraki da aka shigar guda 12,000 kuma an shigar da kararrakin biyan diyya guda 9,000.

Sai dai duk da haka a cewar shugaban Kotun ba ta tsira ba daga fuskantar kalubale domin akwai wadanda suke saka siyasa a ciki da kuma kalubalantar kasancewar kotun yayin da wasu ke kin ba da hadin kai,

Wanda hakan ya sa a yanzu haka akwai wadanda Kotun ke nema ruwa a jallo da yawansu ya kai mutane goma.

Hakan yasa, akwai bukatar a yi amfani da wannan rana domin sake damarar ganin cewa an ci gaba da bi ma wadanda aka zalunta kakkinsu a Hyung Song.

Akwai shugabannin kasashen Afrika da Kotun ke tuhuma da suka hada da shugaban Sudan Umar Hassan al Bashir da Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da kuma tsohon shugaban Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo.

A taron kasashen Afrika da aka gudanar da Addis Ababa, Firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya zargi Kotun da nuna wariya saboda yadda ta ke farautar shugabannin kasashen Afrika fiye da sauran kasashen duniya.

Kasashen da Kotun ta kaddamar da bincike daga rikice rikicen da suka faru sun hada da Uganda da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da Kenya da Libya da Cote d ‘Ivoire da Sudan da Mali. Kuma Kotun tace ta kaddamar da bincike a kasashe da suka hada da Afghnistan da Georgia da Guinea da Colombia da Honduras da Korea da kuma Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.