Isa ga babban shafi
Amurka

An tuhumi Snowden da laifin fallasa sirrin Amurka

Gwamnatin Amurka, ta sanar a hukumance cewa tana tuhumar Edward Snowden wanda kwararre ne a aikin tara bayanan asiri, tare da kira ga Hong Kong ta ci gaba da tsare shi saboda binciken da ake gudanarwa a kan sa bayan ya fallasa bayanan sirrin Amurka.

Batun Edward Snowden shi ne ya mamaye kanun labaran jaridun Hong Kong wanda ya fallasa wasu bayanan asirin Amurka
Batun Edward Snowden shi ne ya mamaye kanun labaran jaridun Hong Kong wanda ya fallasa wasu bayanan asirin Amurka REUTERS/Bobby Yip
Talla

Wata majiyar gwmnatin Amurka ta tabbatar da cewa mai shigar da kara na gwamnati ne ya gabatar da wannan batu a gaban wata Kotun Tarayyar da ke jihar Virginia.

Snowden, ma’aikaci ne a wani kamfani mai zaman kansa da ake kira Booz Allen Hamilton, wanda shi kuma ya bayar da shi haya a wani kamfanin ayyukan tsaro da ke Hawaii inda ake zargin cewa a can ne ya sace bayanan asirin na Amurka.

Wannan tonon asirin dai ya kunyata gwamnatin Obama, inda dole sai gwamnatinsa ta fito ta kare bayanan da Snowden ya yada game sauraren zantukan mutane a wayoyin salula da wasu sadarwa a Intanet.

Rahotanni sun ce Snowden ya shaidawa jaridar Guardian yana neman mafaka a Iceland, amma har yanzu ana tunanin yana cikin kasar Hong Kong.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.