Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka za ta janye rabin dakarunta daga Afghanistan amma za ta ci gaba da yaki da Al Qaeda

Shugaban Amurka Barack Obama ya gabatar da jawabin farko ga 'yan kasar tun bayan zaben da aka yi ma sa a wa'adi na biyu, Shugaban ya tabo batutuwa da dama da ya ke shirin aiwatarwa da kuma batutuwan da suka shafi huldar Amurka da sauran kasashen Duniya.

Shugaban Amurka Barack Obama tare da mataimakinsa  Joe Biden da John Boehner a  Washington
Shugaban Amurka Barack Obama tare da mataimakinsa Joe Biden da John Boehner a Washington REUTERS/Charles Dharapak/Pool
Talla

Shugaba Obama ya ce Amurka za ta janye Dakarunta 34,000 daga kasar Afghanistan a shekarar 2014 tare da alkawalin kawo karshen yake yaken da kasar ta shiga a sauran kasashe.

Amurka tana da yawan dakarun 66,000 a Afghanistan, inda Obama ya ke fatar hannunta ragamar tafiyar da tsaro ga Afghanistan.

Wani babban Jami’in Amurka yace ta wayar Salula, Obama ya shaidawa Shugaban Afghanistan Hamid Karzai da Firministan Birtaniya David Cameron da kuma Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel game da kudirin shi na ficewa da dakarun Amurka daga Afghanistan.

Shugaban yace Amurka za ta hada hannu da kawayenta domin ci gaba da yaki da kungiyar al Qaeda, yana mai gargadin yaduwar ayyukan ta’addanci a kasashen Afrika.

Obama yace gwamnatin shi za ta yi kokarin taimakawa kasashen Yemen da Libya da Somalia wajen girka tsaro a kasashensu kamar yadda suka hannu da Faransa wajen yaki da Mayakan Mali.

A jawabin Obama yace za su dauki kwararan matakai akan Korea ta Arewa bayan kasar ta bayar da sanarwar samun nasarar gwada makamin Nukiliyarta.

Mista Obama yace Amurka za ta karfafa huldar kasuwancinta da Tarayyar turai.

Sai dai ‘Yan majalisun Jam’iyyar Adawa ta Republican sun ce kalaman na Obama ba su gamsar ba domin bai tabo hanyoyin magance rikicin kasafin kudin Amurka ba. ‘Yan adawar sun ce Obama yana kambama gwamnatin shi ne tare da fito da hanyoyin da Amurka za ta kashe kudadenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.