Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya sake karbar Rantsuwar Shugabancin Amurka

Yayin da yanzu haka ake bikin rantsar da shugaba Barack Obama wa’adi na biyu a birnin Washington, ana sa ran batun hadin kan kasa, ya mamaye jawabin da zai yi bayan karbar rantsuwar.Tun dai jiya aka rantsar da shugaban a wani kwarya kwaryar bikin da aka yi a fadar shi, inda ake saran zai fuskanci kalubale da dama wajen bunkasa tattalin arzikin Amurka, kawar da banbance banbancen da ya addabi ‘Yan kasar, da kuma dawo da tagomashin Amurka a idan duniya.Ana kuma fatan ganin shugaban ya kare kudirorin shi, da suka hada da inshoran lafiya, janye kasar daga yake yaken duniya, cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin Israila da Palasdinu.A jawabin da yayi a karshen mako, shugaba Obama yace bikin na wanna karo, wata dama ce ta nazarin halayya, da zaman takewar Amurkawa, da kuma nuna son juna kamar yadda aka gina kasar akai.Ba dai kamar yadda aka gudanar da bikin shekaru hudu da suka gabata ba, inda aka samu halartar baki sama da miliyan biyu suka halarci bikin ba, bana ana sa ran mutane kasa da haka ne zasu halarci wannan biki. 

Shugaban Amurka Barak Obama da mai dakin shi Michelle
Shugaban Amurka Barak Obama da mai dakin shi Michelle REUTERS/Doug Mills/Pool
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.