Isa ga babban shafi
Venezuela

An jinkirta bukin Rantsar da Hugo Chavez na Venezuela

Kotun Kolin kasar Venezuela, tace dage rantsar da shugaba Hugo Chavez, a matsayin zababben shugaban kasar da aka shirya, bai saba dokar kasa ba yayin da aka shirya gangami tsakanin magoya bayan shugaban mai fama da rashin lafiya, da kuma masu adawa da shi.

Shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez zaune a fadar gwamnati
Shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez zaune a fadar gwamnati REUTERS
Talla

Alkalin Kotun Luis Estella Morales ce ta bayyana wannan matakin na hadin guiwar Alkalai bakwai da suka dauka kafin Kotun ta tabbatar da shi.

Shugaba Hugo Chavez ya je kasar Cuba wajen neman Magani saboda matsalar Huhu da ya ke fama da ita, wanda hakan ya kai shi ga mika Ragamar mulki ga mukaddashin sa.

Dama dai ana ta rade-radin cewar muddin Shugaba Chavez bai iya karbar rantsuwar kama aiki ba, to lallai ne a sake sabon zabe.

Kundin tsarin mulkin kasar Venezuela dai ya yi tanadin sake sabon zabe idan shugaban da aka zaba ya kasa karba rantsuwa, ko ya mutu kamin kammala wa'adin mulkin sa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.