Isa ga babban shafi
Isra'ila-Masar-Falasdinawa

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki tsakanin Isra'ila da Hamas, Shugabannin Duniya sun godewa Morsi

Majalisar Dinkin Duniya da Gwamnatin Amurka tare da manyan kasashen Duniya sun yaba da matakan cim ma yarjejeniya tagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan kwashe mako ana ruwan wuta. Shugabannin Duniya sun jinjinawa gwamnatin Masar ga irin rawar da ta taka wajen cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.

Wani Bafalsdine a dai dai wuraren da Isra'ila ta kai hare hare a Gaza
Wani Bafalsdine a dai dai wuraren da Isra'ila ta kai hare hare a Gaza REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

Falasdinawa a Gaza sun bayyana farin cikinsu da tsagaita wutar da aka samu tsakanin kungiyar Hamas da Israila. Suna masu fatar samun dawamammen zaman lafiya a Yankin.

Mohammed Morsi wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar Masar karkashin jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta Brotherhood ya ba shugabanin duniya kwarin gwiwar fatar samun nasara a rikicin Isra’ila da Faledinawa duk da hasashen da wasu kasashen yammaci suka yi bayan zaben shi cewar zai iya mara wa Hamas baya.

Masana da dama sun yi hasashen zaben Morsi zai haifar da kazamar danganta tsakanin Isra’ila da Masar. Amma kasar Amurka tana cikin sahun kasashen da suka yaba wa Shugaban.

Falesdinawa kimanin mutane 160 ne aka ruwaito sun mutu a hare haren da Isra’ila ta kai a Gaza da suka hada da babban Jami’in Hamas Ahmad Jabari.

Musayar Wuta

A ranar 14 ga watan Nuwamba ne kasar Isra’ila ta kai hari a Gaza wanda ya kashe Kwamandan Hamas Ahmad Jabari. Kuma tun daga lokacin Isra’ila ta kaddamar da kai jerin hare hare a wurare 1,500.

Kungiyar Hamas kuma ta harba rokoki sama da 1,500 zuwa yankunnan Yahudawa amma Isra’ila ta yi kokarin kare Rokoki 420 daga cikin wadanda Hamas ta harba.

A jiya rokoki 12 ne Hamas ta harba daga Gaza zuwa Isra’ila sa’o’I kafin a cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta, amma Jami’an tsaron Isra’ila sun ce babu hasarar rai ko rauni da aka samu daga harin na Hamas a kudancin Isra’ila.

Akalla Faledinawa 155 ne aka ruwaito sun mutu tun fara sabon rikicin a ranar 14 ga watan Nuwamba amma Yahudawan Isra’ila Biyar ne kacal suka mutu

Wannan sabon Rikicin kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da Isra’ila ke shirin gudanar da zabe a Watan Janairu inda masana ke zargin Benjamin Natenyahu ya kulla kai hare haren ne domin samun farin jinin Yahudawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.