Isa ga babban shafi
Amurka-Falesdinawa

Obama ya jaddada wa Abbas zai Kalubalanci samun ‘Yancin Falesdinu

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya shaidawa shugaban Falesdinawa cewa gwamnatin shi za ta kalubalanci kudirin samun ‘Yancin Falesdiniwa a zauren Majalisar Dinkin Duniya bayan shugabannin biyu sun kwashe lokaci mai tsawo suna muhawara ta wayar Salula.

Shugaban Faledinawa Mahmoud Abbas tare da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya  Ban Ki-moon
Shugaban Faledinawa Mahmoud Abbas tare da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon REUTERS/Keith Bedford
Talla

Kakakin Falesdinawa Nabil Abu Rudeina yace Obama ya shaidawa Abbas Amurka za ta kalubalanci kudirin samun ‘Yancin Falesdinawa.

Tuni dai Shugaban Falasdinawa, Mahmud Abbas, yace zai bukaci babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a watan Nuwamba ya amince da kasar Falasdinu, duk da matsin lambar da suke samu daga wasu kasahsen duniya na kaucewa yin haka.

Duk da Shugaba Abbas bai ambaci sunayen kasashen da ke matsin lamba ba, amma rahotanni na nuna cewar Amurka da Isra’ila sune kasashen da ke kan gaba.

An dade dai Amurka da Isra’ila na hawa kujerar na-ki ga kudirin Falesdinu suna masu neman an koma a teburin sasantawa da aka dakatar shekaru masu yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.